1 John 3

1Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu ‘ya’yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba. 2Kaunatattu, yanzu mu ‘ya’yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa’adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake. 3Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki.

4Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari’a kenan. Gama zunubi ketare shari’a ne. 5Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi. 6Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi.

7‘Ya’yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali. 8Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis.

9Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah. 10Ta haka ne ake bambanta ‘ya’yan Allah da ‘ya’yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan’uwansa.

11Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu, 12ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan’uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan’uwansa kuma masu adalci ne.

13Kada kuyi mamaki ‘yan’uwana, idan duniya ta ki ku. 14Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar ‘yan’uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne. 15Dukkan wanda yake kin dan’uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai.

16Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda ‘yan’uwamu. 17Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan’uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa? 18‘Ya’yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya.

19Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa. 20Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome. 21Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah. 22Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi.

23Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka. Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.

24

Copyright information for HauULB